29 Yuli 2020 - 13:45
‘Yan Adawan Mali Sun Yi Fatali Da Bukatun ECOWAS

‘Yan adawa a kasar Mali, sun yi watsi da shawarwarin da kungiyar ECOWAS, ta gabatar na warware rikicin siyasar kasar.

ABNA24: A wata sanarwa da suka fitar ‘yan adawan na Mali, sun ce har yanzu suna kan bakarsu, ta neman shugaban kasar Ibrahim Bubakar Keita ya yi murabus daga kan mulki.

A jiya ne yayin wani taronsu na gaggawa shugabannin kungiyar ta ECOWAS, suka gabatar da wasu shawarwari da suke ganin zasu taimaka wajen kwatar da hankali a kasar ta Mali, da sukaha da soke zaben ‘yan majalisar dokokin da ake ganin yana cike da kura kurai, da kuma kafa gwamnatin hadin kasa wacce ta kunshi ‘yan adawa da kuma kungiyoyin fara hula.

Kungiyar ta ECOWAS, ta yi barazana a karon farko da amfani da takunkumi kan wadanda suke kawo cikas a yunkurin sasanta rikicin siyasar kasar ta Mali.

A wani labarin kuma kwamitin tsaro na MDD, ya bukaci dukkan bangarorin kasar ta Mali, dasu mutunta bukatun da shugabannin na ECOWAS suka gabatar ba tare da wata wata ba, domin shawo kan rikicin kasar

342/